Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurkawa sun yi bikin zagayowar ranar samun 'yancin kai


Wasu daga cikin wasan hasken wuata na ranar samun 'yancin kan Amurka
Wasu daga cikin wasan hasken wuata na ranar samun 'yancin kan Amurka

Miliyoyin Amurkawa ne su ka taru a wurare dabam dabam don kallon

Miliyoyin Amurkawa ne su ka taru a wurare dabam dabam don kallon wasan hasken wutar da aka saba yi, na zagayowar ranar samun ‘yancin kan kasar da aka yi da daren jiya Labara.

Dubun dubatan mutane sun daure wa tsananin zafi a birnin Washington don halartar bukukuwan wakoki da wasan hasken wuta na shekara-shekara a birnin Washington – a sa’ilinda kuma su ke ta kallo sama don doki.

Hasken wasan wutar ya yi ta haskaka sararin sama bisa tsohon fagen dagar yakin 1812 da kuma yakin basasar Amurka. An kuma gudanar gawurtattun wasannin hasken wuta a tsohon babban birnin Amurka, wato Philadelphia da kuma birnin New York.

Kafin nan, da safiyar jiya Laraba, Shugaba Barack Obama ya marabci wasu dakarun Amurka 25 bayan sun dau rantsuwar zama ‘yan kasa a Fadar Shugaban Amurka ta White House. Mr Obama ya ce zuwan baki na sa Amurka ta kara karfi. Mutane 25 din da su ka yi rantsuwar yin biyayya ga sabuwar kasar tasu sun fito ne daga kasahen Mexico da Colombia da Nijeriya da kuma Rasha.

Bukin na bana shi ne zagayowa ta 236 ta samin ‘yancin kasar daga kasar Burtaniya.

XS
SM
MD
LG