Wannan kira da ‘yan jam’iyyar Dimokrat suka yi, na zuwa ne bayan da aka gano cewa a bara Sessions ya gana da jakadan Rasha na Amurka.
A lokacin ya na Majalisar Dattawan Amurka, Sessions ya goyi bayan shugaba Trump yayin yakin neman zabe, inda ya rike mukamin mai ba da shawara a kwamitin yakin neman zabe.
A lokacin da ‘yan majalisa suke tantance shi a bayan da shugaba Trump ya mika sunansa a matsayin wanda zai jagoranci hukumar shari’ar kasar, an tambayi Sessions ko mai zai yi idan aka samu hujjar cewa wani na hannun daman Trump ya tuntubi Rasha?
Sai ya ce: “A wani lokaci ko kuma a wasu lokuta , akan kira ni da sunan dan-baranda a yakin neman zabe, kuma ni ban yi wata ganawa da Rasha ba, Saboda haka ba zan iya cewa komai a kai ba.”
Shi dai Sessions ya taba ganawa da Jakadan Rasha Sergie Kislyak a watan Yuli a gefen babban taron jam’iyyar Republican, sannan sun sake haduwa a watan Satumba a ofishinsa dake majalisar dokokin Amurka.
Sai dai mai Magana da yawun ma’aikatar shari’ar Amurka, Sarah Isgur Flores, ta ce Sessions bai yi karya a bayanin da ya yi wa kwamitin ‘yan majalisar da suka tantance shi.
Facebook Forum