Shugaban Amurka Donald Trump ya ce kula da lafiyar Amurkawa, shi ne zai zamanto muhimmin batu a kokarin da gwamnatinsa ke yi na ganin an dawo da harkokin yau da kullum a kasar.
Shugaban na Amurka tare da kwamitin da ya kafa na yaki da cutar coronavirus, sun fara fitar da tsare-tsaren da za a bi wajen maido da al’amuran yau da kullum a kasar, inda suke fatan ganin ma’aikata sun koma bakin aiki.
Ya kara da cewa, akalla jihohi 29 sun nuna sha’awarsu ta ganin an dawo da harkokin yau da kullum nan ba da jimawa ba, sai dai ya kara da cewa, ya ragewa gwamnonin jihohin da na shugabannin kananan hukumomi su yanke shawarar maido da harkokin yau da kullum a yankunansu.
Wannan sanarwa ta Trump na zuwa ne, sa’o’i bayan da Mai Mukamin Magajin Garin birnin Washington, Muriel Bowser, ta kara tsawaita dokar hana zirga zirga har nan da ranar 15 ga watan Mayu, inda ta ce matakin zai ci gaba da wakana, har sai an ga adadin sabbin masu kamuwa da cutar ya yi kasa cikin mako biyu
Adadin masu kamuwa da cutar ta COVID-19, na ci gaba da karuwa a Amurkan, inda yawansu ya kai dubu dari 667 izuwa ranar Alhamis, kana kusan mutum dubu 35 sun mutu a cewar hukumar lafiya duniya WHO.
Facebook Forum