Wata ma’aikaciyar kiwon lafiya ko Nurse, wacce hukumomin jihar New Jersey suka killace ta ala tilas, saboda zargin tayi jinyar wadanda suka kamu da Ebola, yanzu an sallameta, a dai dai lokacinda cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Amurka, ta bayyan sabbin matakai da ake bukatar ma’aikatan kiwon lafiya da suka akan wadanda suka dawo daga kasashen Afirka masu fama da cutar.
Cibiyar hana yaduwar cututtukar wacce ake kira CDC a takaice, tayi kira ga ma’aikatan kiwon lafiya da suka dawo daga jinyar masu fama da cutar Ebola a Afirka, su killace kansu a gidajensu. Hukumar tace babu bukatar ma’aikatan su kadaice, maimakon haka hukumomin Amurka zasu rika sa musu idanu.
Ranar Jumma’a ce Nurse Kaci Hickox, ta dawo Amurka daga aikin jinyar wadanda suke fama da cutar Ebola a yammacin Afirka. Kaci ta zama mace ta farko da dokar da jihar New Jersey ta kafa wacce tace tilas a killace irin wadannan ma’aikata na tsawon kwanaki 21 ta fara aiki akanta. Bayan gwajin da aka yi mata, ba’a sami Kaci da cutar ba, kuma tayi barazanar zata kalubalanci wannan dokar a gaban kotu.