Wani mashawarci ga gwamnatin Amurka ta Barack Obama yace Amurka zata dora akan nasarar da ta samu na hallaka madugun al-Qaida, ta ci gaba da wargaza kungiyar tashi a ko ina take a duniya.
A yau ne babban jam’in cibiyar yaki da ta’addanci na Amurka John Brennan yake fada akan shirin “Today Show” na gidan telebijin na NBC cewa kashe Bin laden daya ne daga cikin matakan da gwamnatin ta Amruka ke dauka na fattataka kungiyar ta al-Qaida.
Jami’in yace wani dukan da al-Qaida zata sha yana kan hanya – daga tarin assiranta da aka samu a gidan shi bin Laden din, inda aka kai mishi farmakin da ya hallaka shi.
Ta wani gefen, Amurka na jan kunnen ‘yan kasarta dake a kasashen ketare da su zauna cikin hattara da kulawa saboda tsoron ramuwar gayya akan kisan da Amurka din ta yi wa madugun al-Qaida, Osama Bin Laden.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurkan Amurka tace yanzu haka an dauki tsaurarn matakan tsaron lafiyar manyan opisoshi da ma’aikatun Amurka dake kasashe daban-daban, har ma ana tunanin kila wasunsu a dakile su kwata-kwata ko a jinkirta bude su ga jama’a.