Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Umurci 'Yan Twayen Syria Su Fice daga Aleppo


John Kerry sakataren harkokin wajen Amurka wanda ya bada umurnin ficewar shekaran jiya.
John Kerry sakataren harkokin wajen Amurka wanda ya bada umurnin ficewar shekaran jiya.

Jami’an masu hamaiya a kasar Syria sunce yan tawayen da aka fi karfin su, wadanda suke fafatawa da sojojin gwamnati wadanda ke samun taimakon Rasha a gabshin birnin Aleppo sun samu shawara daga Amirka cewa su bi sahun farar hula da suke ficewa daga birnin karkashin wani shirin Rasha na barin farar hula su fice, suma su fita daga birnin.

Jiya Lahadi da dare kamfanin dilancin labarun Reuters ya bada rahoton wannan shawarar da Amirka ta gabatar, yana mai fadin cewa har yanzu kungiyoyin yan tawaye basu maida martini ga wannan tayin ba. Haka kuma rahoton yace Rasha ta dage akan cewa ba’a cimma yarjejeniya ta karshe ba tukunan.

Idan dukkan bangaroi sun yi na’am da yarjejeniyar, yarjejeniyar zata share fagen kawo karshe fafatawar shekaru hudu a birnin Aleppo da kuma kawo karshen kusan watani uku na munanan hare haren da sojojin Rasha dana Syria suke ta kaiwa birnin da jiragen saman yaki da kuma bindigogin igwa.

A lokacinda ake ganiyar kai hare haren, ma’aikatan jakadanci sun kiyasta cewa kimamin farar hula dubu maitan da hamsin da aka yiwa kawanya basu da sukunin samun taimakon kayayyakin agaji na jin kai da suke bukata ruwa a jallo, kuma yawancin su tsoro ya hana su ficewa daga birnin

XS
SM
MD
LG