Wani farmakin da Amurka ta kai da jiragen yaki sun halaka mayakan al-Qaida su fiye da dari, a wani sansanin horaswa ta sojoji a Syria, kamar yadda wani jami'in ma'aikatar tsaron Amurka ya gayawa Muriyar Amurka, a jiya jumma'a, a wani babban farmaki kuma na karshe da sojojin na Amurka suka kai kan 'yan ta'adda karkashin gwamnatin Obama.
Jirgin yaki kirar Beoing, samfirin B-52, ya auna hari kan sansanin a yammacin Alhamis, agogon yankin. Sansanin yana daga yammacin birnin Aleppo, a lardin Idlib, inji jami'in tsaron.
A baya, wata kungiyar mayakan sakai da ake kira Jabhat Fatah al-sham, wacce aka fi sani da sunan Al-Nusra, kamin daga baya kungiyar al-Qaida ta fara amfani da sansanin a zaman wurin horasda mayakanta.
"wannan ai sanannan wuri ne na horo kusan shekaru biyu," inji jami'in.
Illahirin mayakan suna cikin wani gini daya lokacin da aka kai farmakin,kamar yadda jami'in ya fada.
Farmakin na Syria, yana zuwa ne sa'o'i bayan da wasu jiragen yaki biyu samfirin B-2 suka kashe fiye da mayakan sakan ISIS 80 a sansanoni biyu dake kudu maso yammacin Sirte a Libya.
Da yake magana a ranarsa ta karshe a ofis ranar Alhamis, sakataren tsaron Amurka Ash Carter, ya gayawa manem labarai a Pentagon cewa, mayakan sakan da aka kaiwa hare haren sun hada da "masu shirin kai hare hare, dake tsara yadda zasu kai farmaki akan kawayen Amurka a Turai."