Gwamnatin Amurka ta kara kudin samun izinin shiga Amurka, biza, matakin da ta baiyana da rama wa kura aniyarta kan yadda gwamnatin Najeriya ta kara kudin shigowa Najeriya ga Amurkawa.
Ofishin jakadancin Amurka a Abuja ya fitar da sanarwar ta karin da kebantacce ne daga asalin kudin biza da ake caji da zai shafi ‘yan Najeriya da ke son shigowa Amurka daga kowace kasa ta duniya.
Sanarwar ta kara da cewa tun farkon bara gwamnatin Najeriya ta kara kudin shigowa kasar ta ga Amurkawa, kuma Amurka ta dau matakan jan hankali don janye karin amma hakan bai yiwu ba har bayan watanni 18.
Sai dai karin da Amurka ta yi ya kama daga dala 80 zuwa dala 303.
Bashir Baba, wani tsohon jami'i a ma’aikatar wajen Najeriya, ya ce ba wani abun tada hankali kan karin don dama zuwa Amurka na wadanda su ka shirya ne.
Kazalika jami’in walwala na jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Ibrahim Masari, ya ce hakan bai daga mu su hankali ba don bai shafi kasashen da talakawa su ke zuwa don ibada ba.
Ba a taba samun musayar kausasan kalamai tsakanin Najeriya da Amurka ba don ba mamaki yadda kasashen biyu ke da muradu na musamman a huldarsu ta kasuwanci da diflomasiyya.
Wani rahoto ya bayyana cewa a shekarar 2017 kadai 'yan Najeriya sun kashe Naira biliyan 17 wajen neman biza ta shiga Amurka.
Kazalika kudin ko da mutum bai samu nasara ba ba za a mayar ma sa da su ba.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja:
Facebook Forum