Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tilas Amurka Ta Tsaida Karbar 'Yan Somalia-Donald Trump


Donald Trump da mataimakinsa Mike Pence
Donald Trump da mataimakinsa Mike Pence

Dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican Donald Trump ne yayi wannan kira a Portland Maine.

Dan takarar shugabancin Amurka Donald Trump ba bako bane wajen tada rikici a zaben bana, inda ya tabo musulmi da 'yan kasar Mexico. Ranar Alhamis ya auna 'yan kasar Somaliya dake Amurka.

Da yake magana a wani gangamin yakin neman zabe a birnin Portland dake jihar Maine, Trump yace akwai bukatar Amurka ta tsaida karbar 'yan gudun hijira daga Somalia. Yace Amurka ta bude kofarta ga kasashe da suke fama da rashin tabbas,domin tana karbar "kare da fatan rago."

Dan takarar na jam'iyyar Republican ya bayyana shakku kan hanyoyin da hukumomi suke bi na tantance wadannan mutane. Yace saboda yawan rashin ayyukan yi tsakanin irin wadannan 'yan gudun hijira daga Somalia, yana da sauki ISIS ta kwashe su sojan haya.

Shugabannin al'umar Somali a Amurka kamarsu Ahmed Shu'ayb sun bayyana bakin ciki kan kalaman Mr. Trump wadda suka ce zai haifarda husuma da tsangwama ga al'umar Somalia wadanda suke zaune cikin lumana.

Trump ya bada misali da dan wani kasar Somaliyan, wanda aka yankewa hukuncin daurin shekaru 30, saboda samunsa da laifin shirin kai hari kan shirye shiryen kirsimeti a shekara ta 2010.

Shima da yake maida martani dan Majalisar wakilan Amurka daga jihar Minnesota Mr. Ellison, musulmi na farko a majalisar, ta shafin Twitter, ya gayawa Donald Trump, "ina so na maka magana kan maganganu na rashin hankali da kake yi kan jihata da kuma wadanda suke mazabata."Al'umar baki su suke karfafa Amurka, koda me menene 'yan raba kawunan jama'a kamarka suka ce."

XS
SM
MD
LG