Bayan da kamfanin jiragen fasinjar kasar Etihad ya aiwatar da sabbin matakan tsaro.
Dokar ta fara aiki ne cikin watan Maris wacce ta shafi jirage da suke zuwa Amurka kai tsaye daga tashar jiragen sama 10 a yankin Gabas ta tsakiya, saboda damuwar da jami'an Amurka suke da ita cewa akwai yiyuwar 'yan ta'adda su boye bama bamai cikin na'urorin masu kwa-kwalwa.
Kamfanin Etihad wanda yake jigila 45 ko wani mako daga Abu Dhabi zuwa Amurka, yayi marhabin da wannan mataki.
Wani kakakin ma'aikatar tsaron cikin gida ta Amurka ya yabawa kamfanin jiragen saman saboda sabbin matakai da ya dauka, wadanda ba'a bayyana su ba, ya kara da cewa "matakin zai kasance abun koyi ga jirage da suke zirga-zirga cikin gida da kuma ketare."
Har yanzu dokar tana ci gaba da aiki kan jiragen sama da suke tashi kai tsaye zuwa Amurka daga tashoshin jirgin-sama a Kuwait, da Jordan, da Masar, da Turkiyya, da Saudiyya, da Morocco, da Qatar, da kuma Dubai
A jiya lahadi ne Amurka ta dage dokar hana shiga cikin jirigin sama da komputar hanu daga Abu Dhabi, helkwatar hadaddiyar daular kasashen larabawa
WASHINGTON DC —
Facebook Forum