Jami’an Amurka da na Jamhuriyar Nijar sun tsawaita tattaunawar da suke yi a hukumance kan ficewar sojojin Amurka daga kasar ta Nijar har zuwa ranar Juma’a.
Mataimakin Sakataren tsaro a fannin na musamman Christopher Maier da Laftanar Janar Dagvin Anderson, wanda shi ne Darekatan dakarun hadin gwiwa sun tattauna da wakilan sabuwar gwamnatin sojin Nijar a Niamey a ranakun Laraba da Alhamis.
Muryar Amurka ta ruwaito cewa tattaunawar ta kawo karshe a ranar Alhamis, amma jami’an Amurka da Na Nijar sun yanke shawarar tsawaita zaman har zuwa ranar Juma’ar da ta gabata a cewar wani jami’in tsaron Amurka wanda ya nemi a sakaya sunansa.
Bangarorin biyun sun yanke shawarar Amurka za ta janye dakarunta cikin watannin masu zuwa ba da bata lokaci ba.
Dandalin Mu Tattauna