Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya ce Amurka tana tunanin takaiata ko aza takunkumin sayen man fetur daga Venezuela a kokarin ta na matsawa kasar.
Ya bayyana hakan ne a zaman tattaunawar da suka yi da manyan kasar Argentina jiya Lahadi a ziyarar da ya kai kasar. Ya ce suna ganin yin hakan zai taimaka wajen tilastawa kasar ta gudanar da sahihin zabe mai adalci..
Amman Tillerson ya kara da cewa yana so a samo hanyoyin da zasu rage illar da takunkumin zai haifar ga kamfanonin man Amurka da wadansu kasashen da suka dogara ga samun mai daga kasar ta Venezuela.
Venezuela ita ce kasa ta uku mafi da ta fi sayar wa Amurka man fetur, kuma kamfanonin mai na Amurka sun ce hana shigo da man fetur daga kasar zai shafi ma'aikata a nan Amurka, kuma zai sa farashin man ya yi tashin goran zabi.
Facebook Forum