Amurka ta yi kira ga Tarayyar Turai da ta kakaba takunkumi ma kungiyoyi da daidaikun mutanen da ke da hannu a shirin makamai masu linzami na Iran, bayan da Iran ta ce ta yi nasarar kaddamar da wani tauraron dan adam na soji.
Amurka ta kuma yi kira ga dukkannin kasashe da su yi aiki da takunkumin hana sayen makamai da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba ma Iran, ta ce kaddamar da wannan makami da Iran ta yi shaida ce cewa shirin nukiliyar Iran fa “ba na zaman lafiya ba ne kuma ba na farar hula ba ne.”
“Amfani da irin wannan na’ura ta kaddamarwa da kuma sauran wadanda su ka gabaci wannan na tafe da fasahar da ke da nasaba da makamai masu linzami da kuma wadanda kan iya rikidewa zuwa na makamai masu linzami, ciki har da masu cin dogon zango irin masu zuwa kasa da kasa (ICBM a takaice). Babu wata kasar da ta kuduri aniyar mallakar ICBM fa ce ta na da niyyar mallakar makamin nukiliya,” a cewar Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo a wata takardar bayani ta jiya Asabar.
Facebook Forum