Ashton ta bayyana zaben Shugaban kasar Ukraine da za a gudanar ran 25 ga watan mayu din da cewa mai matukar muhimmanci ne ga kokarin kawo kwanciyar hankali. Ta ce mutanen Ukraine ne za su yanke shawara kan ko mecece Ukraine da kuma abin da za ta kasance a gaba.
Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov ya fadi jiya Talata cewa akwai waswasi game da sahihancin zaben saboda matakan soji da gwamnatin Ukraine ta dauka a gabashin kasar kan 'yan aware magoya bayan Rasha.