Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AMURKA: Daga Yanzu Duk Wanda Aka Samu da Laifin Yin Lalata da Yara Kanana Za'a Bashi Fasfo Na Musamman


 Rex Tillerson, sakataren harkokin wajen Amurka
Rex Tillerson, sakataren harkokin wajen Amurka

Daga yanzu za a rika bai wa mutanen da aka masu rijista a matsayin masu yin lalata da yara kanana paspo na musamman a nan Amurka kafin a barsu su yi tafiya zuwa kasashen waje.

A jiya Alhamis, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce za ta fara soke tsohon paspo din irin wadannan mutanen, inda za a nemi su sake neman sabon paspo, wanda zai nuna wata “fitacciyar alama” da za ta nuna cewa sun taba lalata da kananan yara.

Wannan mataki na zuwa ne bayan wata doka da aka amince da ita a bara.

Wadanda aka samu da wannan laifi, za a basu wani paspo wanda a shafinsa na baya, za a rubuta “an taba samun wanda ke rike da wannan paspo din da laifin yin lalata da kananan yara, kuma hukuma na sane da shi a matsayinsa na mai lalata da yara, (kamar yadda dokar Amurka ta tanada.)

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce daukan wannan mataki ya samo asali ne tun bayan da aka samu wani mutum da aka taba samu da laifin yin lalata da kanana yara, wanda ya yi garkuwa tare da kashe wata yarinya ‘yar shekara bakwai mai suna Megan Kanka a jihar New Jersey a shekarar 1994.

Wannan al’amari shi ya sa aka bude ofisoshin yin rijistar masu yin lalata da yara kanana da dama.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG