Amurka da kasar Saudiya sun kaddamar da karin hare hare kan muradun kungiyar ISIS kusa da garin Kobani a Syria a jiya Litinin, yayinda mayakan sakan kurdawa da na ISIS suke gwabza kazamin fada domin iko kan garin.
Daga Turkiyya ana hango hayaki bakikkirin yana tashi a garin na Kobani. Wani jami’in garin yace mayakan sakan ISIS sun yiwa garin zobe ta kowane kusurwa in banda ta arewaci a mashigin da yake kusa da Turkiyya ba. Ya bayyana fargabar cewa mayakan zasu toshe garin baki daya idan har suka kewaye shi ta ko ina.
Helkwatar rundunar mayakan Amurka ta ce jiragen yakin Amurka da
na Saudiya sun kai hare hare har sau hudu a a kudu maso yammacin Kobani suka lalata wani wurin da suke shirya kai hare hare da kuma wata cibiyar bindigar da take sarrafa kanta. Wasu hare haren kuma sun afkawa wasu cibiyoyi a arewa maso gabashin garin, ciki harda wasu gine gine biyu da ISIS take amfani dasu.
Ahalinda ake ciki kuma iyayen wani ba Amurke da kungiyar ta ISI take garkuwa dashi sun gayawa wata tashar talabijin ta Amurka cewa ba zasu iya cika sharuddan da kungiyar ta ISIS ta gindaya ba domin dansu da take garukwa dashi kuma take barzanar zata sare kansa.