Shugaban Amurka Barack Obama yace farmaki ta kasa a Syria ba "zai yi aiki ba."
Shugaban na Amurka ya gayawa manema labarai jiya jumma'a cewa kodashike Rasha ta shigo cikin rikicin, kuma Iran tana kara turori sojoji, hakan ba zaiyi aiki ba "domin suna kokarin su goyi bayan gwamnatin da a idanun galibin 'yan kasar ba halattacciya bace."
Kalaman na Mr. Obama sunzo ne a dai dai lokcinda Amurka da Rasha suka cimma daidaito a ka'idance cewa zasu nisance jiragen juna, yayinda kasashen duka biyu suke kai farmaki ta sama a Syria. Obama yace ta wannan kadai kasashen biy suka cimma matsaya tunda Rasha ta fara amfani da karfin soji a karshen watan satumba wanda ya janyo tankiya.
Dakarun Syria a safiyar jiya jumma'a suka fara kai farmaki a lardin Aleppo, a wani mataki da suka dauka a baya bayan nan na sake kwaro kasa, a gwabzawar kasar take yi da kungiyar ISIS da kuma wasu kungiyoyin 'yan tawayen kasar.