Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Kungiyar Tarayyar Turai Sun Cimma Matsaya Kan Kudin Fito


Gwamnatin Amurka da kungiyar tarayyar Turai sunce sun cimma matsaya akan harkokin cinikayya, tare da alkawarin ba zasu tsawwala ma juna ba akan Karin kudin fito.

shugaban Amurka da na kungiyar tarayyar Turai, bayan wata ganawar da suka yi na tsawon sao'i 3 a fadar White House, sun bayyana cewa sun cimma matsaya akan ba zasu kara wa juna harajin cinikayyar dake tsakanin su ba, domin sunyi la'akari da cewa kasuwancin dake tsakanin su yana da dinbin tasiri ga sauran kasuwannin duniya.


Shugaba Trump yace "Yau mun cimma matsaya domin muyi aiki tare domin kaiwa ga nasarar ganin bamu kara wa juna haraji ba koda na sisin kwabo ne akan kasuwancin masana'antun mu.


Shugaban Trump ya bayyana haka a fadar White House lokacin da yake tare shugaban kungiyar Jean Claude Junker."Yace haka kuma zamu yi aiki domin ganin mun rage shingen dake tsakanin mu, tare da kara harkokin kasuwancin mu akan abubuwan da suke da nasaba da

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG