Sanarwar da aka fitar jiya Talata, ta ce sakataren ma’aikatar kudi Steven Mnuchin da jami’in cinikayya Robert Lighizer za su gana da mataimakin Firimiya Liu He a birnin Beijing ranar 30 ga watan nan na Afrilu.
Bangarorin biyu dai za su tattauna kan batutuwan da suka hada da fasahar da juna ke da su da tilasta musayar fasaha da kuma kudaden haraji da ba a karba da kuma kayayyakin amfanin gona.
Fadar White House ta ce mataimakin Firimiya Liu shine zai jagoranci tawagar jami’an China zuwa Washinton a makon gaba domin ci gaba da tattaunawar ranar 8 ga watan Mayu.
Amurka da China sun sha yin tattaunawa tun farkon shekarar nan domin sasantawa kan rikicin cinikayya da ya fara tun shekarar da ta gabata, lokacin da shugaban kasa Donald Trump ya saka harajin Dala biliyan 250 akan wasu kaya da China ke shigarwa Amurka. Haka kuma ita kanta China ta mayar da martani ta hanyar ‘kara haraji akan kayan Amurka har na Dala biliyan 110.
Facebook Forum