'Yan gudun hijira daga jihohin Yobe da Borno sun fantsama cikin jihar Adamawa sakamakon hare-haren 'yan Boko Haram inda a Bole cikin karamar hukumar Yola ta rungumi 'yan gudun hijiran da hannuwa biyu.
Hare-haren 'yan Boko Haram ya sa dubun dubatan 'yan gudun hijira daga jihohin Yobe da Borno sun fantsama cikin jihar Adamawa domin neman mafaka.
A wasu wuraren 'yan gudun hijiran kan fuskanci matsaloli daga wasu al'ummomi amma a yankin Bole a karamar hukumar Yola ta kudu lamarin ba haka yake ba. Al'ummar Bole ta rungumi 'yan gudun hijiran da hannu biyu.
Wata tace daga inda suka fito 'yan Boko Haram sun yanka mijinta amma ta samu ta gudo da yaran. Wata kuma tace gidansu aka kone gaba daya.
Ado Abdulmunmuni Bakare mai kula da yankin Bole ya bayyana yadda suke rike da 'yan gudun hijiran. Yace maimakon su samar da wani wuri na musamman mutanen garin suke roko su ajiye 'yan gudun hijiran a gidajensu. Wasu kuma suna zaune a gidajen da ba'a gama ginasu ba. Idan an samu irin gidajen da ba'a gaba ginasu ba sai a nemi mai gidan a rokeshi.
Wata da take tallafawa 'yan gudun hijiran tace wadanda ke cikin gidanta daga Maiduguri da Potiskum suka fito. Tace da suka zo anguwarsu sun rarrabasu cikin gidajensu suna zaune suna kula da lafiyarsu. Ta nemi a taimakesu ta gefen ruwa da abinci da suturar da zasu sa. Wadanda suke da ciki suna bukatar a taimaka masu idan lokacin haifuwarsu yayi.
Sakataren hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Adamawa Alhaji Hamma Haruna Foro ya yaba da irin taimakon da al'ummar Bole ke ba 'yan gudun hijiran. Yace banda ajiyesu a gidajensu sun kuma basu filayen noma. Sabili da haka ya bukaci sauran al'ummomi da su yi koyi da Bole
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.