Uwargidan tsohon shugaban Amurka marigayi Ronald Reagan, watau Nancy Reagan ta rasu.
Uwargidan shugaban Amurka na 40, ta mutu ne yau Lahadi tana da shekaru 94.
Matsaloli masu alaka da zuciya sune suka haddasa mutuwarta.
Wata mujallar harkokin nishadi da ake kira TMZ ce ta fara bada labarin a shafinta na internet. Nancy Reagan tana da zama a wata unguwar da ake kira Bell-Air, a jihar Califronia.
'Yan wasan kwaikwayo, mata mijin, sun yi aure fiyeda shekaru 50, mijinta ya shugabanci Amurka daga 1981-1989.
A matsayinta na 'yar wasan kwaikwayo rukuni na "B", ta hadu da Ronald Reagan ne a wajajen 1940, wanda shima dan wasan kwaikwayo ne. A lokacin ana kiranta Ann Francis Robbins,-tana amsa sunan Nancy Davis, a cikin wasan kwaikawayon. Suka yi aure a 1952.
Maigidanta Ronald Reagan, yayi gwamnan jihar California daga 1967 zuwa 1975. Bayan da ya kasa samun takarar shugabancin Amurka 1976, daga bosani ya sami nasara 1980.
A zamanin mijinta yana shugaban Amurka, ta jagoranci yaki da sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi, musamman fodar iblis.