Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alkali Mai Bincike Ya Jefa Tsohon Ministan Cikin Gidan Nijer A Kurkuku


Hukumomin Jamhuriyar Nijer sun cafke tsohon Ministan Cikin Gida bugo da kari tsohon Jakadan kasar a Chadi, Ousman Cisse,  saboda zarginsa da hannu a yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a ranar 31 ga watan Maris na 2021.

Lamarin dai ya fara daukar hankalin ‘yan siyasa da ‘yan rajin kare hakkin dan adam.

Ainihi Hukumar Jandarmomi ta Kasa ce ta kama tsohon Ministan Cikin Gida, Ousman ibrahim Cisse, a karshen makon jiya wace bayan zaman saurare na wasu awoyi ta gabatar da shi a gaban alkali mai bincike, inda a karshe aka wuce da shi gidan yarin Birnin N’gaoure dake a km 100 kudu masu gabascin birnin Yamai.

Cisse Ousman Ibrahim, wanda a watannin baya aka tsige shi daga mukaminsa na Jakadan Nijer a kasar Chadi, na daga cikin wadanda ake zargi da yunkurin kifar da mutumin da ya ba shi wannan mukami wato Shugaba Mahamadou Issouhou. Hasalima hukumomi na cewa a ofishinsa na birnin N’djamena aka tsara juyin mulkin na 31 ga watan maris na 2021.

Lauyan dake kare tsohon ministan, Me Mohamed Hamani Maiga Salim, ya nuna rashin jin dadi dangane da yanayin da aka kama shi.

Ya ce ba a bi ka’ida ba, sannan ya ce sai a lokacin da ake shirin kai shi kurkuku aka sanar da shi cewa ana zarginsa da hannu a yunkurin juyin mulki. Yanayin jikinsa shi ma wata matsala ce dake bukatar dubawa. Dalilin kenan da ya bukaci a kai shi kurkukun da zai iya samun ganin likita idan bukata ta taso. Sai dai ba a saurare shi ba.

Tsohon shugaban hukumar ‘yan sanda na kasa baki daya, Ousman Cisse, ya yi Ministan Cikin Gida a zamanin gwamnatin mulkin sojan da ta hambarar da shugaba Tanja Mamadou a karkashin jagorancin Commandant Salou Djibo.

Tuni dai wannan batu ya fara daukar hankulan bangarorin siyasar wannan kasa. Shugaban jam’iyar Moddel Ma’aikata, Tahirou Guimba, na mamakin wannan dambarwa.

Shugaban gamayyar kungiyoyin ROADD masu kare hakkin dan Adam da tabbatar da dimokradiya, Son Allah Dambaji, ya gargadi mahukunta akan bukatar gudanar da komai na wannan badakala ta hanyar mutunta abubuwan da doka ta yi tanadi, wato idan da laifi a yi hukunci, idan kuma babu shi a nan ma a bi doka.

Da daren Talata wayewar Laraba 31 ga watan Maris na 2021 ne wasu sojoji suka bude wuta a kewayen fadar Shugaban kasar Nijer da nufin kifar da shugaba Issouhou Mahamadou kwanaki 2 kafin a rantsar da mutumin da zai gaje shi wato shugaba Mohamed Bazoum.

‘Yan makwanni bayan haka binciken hadin gwiwar hukumomin Nijer da Jamhuriyar Benin ya bada damar cafke wasu daga cikin jagororin wannan yunkuri, captaine Sani Gourouza, da lieutenent Abdourahmane Morou. Ana hasashen gurfanar da su a nan gaba kadan a kotun hukunta laifukan soja.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG