Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alkalan Sudan Ta Kudu Sunce Babu Ja Da Baya a Zanga-zangar Da Suke


Shugaba Salva Kiir
Shugaba Salva Kiir

A yau Juma’a ne Alkalai a Sudan ta Kudu suka ce, duk da cewa shugaban ‘kasa Salva Kiir ya kori abokan aikinsu 14, zasu ci gaba da gudanar da zanga-zanga har sai an biya musu bukatunsu.

Alkalan dai sun fara yajin aiki tun ranar 1 ga watan Mayu, suna bukatar shugaba Kiir ya yi musu karin albashi, ya kuma aiwatar da wasu sauye-sauye a fannin aikinsu, ya kuma cire shugaban alkalai Chan Reec Madut daga aikinsa saboda watsin da yayi da bukatun na su.

A wani taron manema labarai da aka yi a birnin Juba, Bold Lul Wang, mai wakiltar alkalan na Sudan ta Kudu, ya ce Alkalan sunyi matukar tabuwa da jin abin da Kiir yayi, na yin amfani da ikonsa na shugaban kasa ya kafa doka ranar Laraba.

Wang ya ce Alkalan Sudan ta Kudu sun gudanar da wani taron gaggawa yau Juma’a a Juba da sauran garuruwa a fadin kasar domin tattaunawa kan korar da aka yiwa wasu alkalai.

Alkalan dai na kira ga shugaban kasar cikin gaggawa da ya dawo da wadanda ya kora, ya kuma biya musu bukatun da suke nema. Ya kuma ce baki ‘daya alkalan suna goyon bayan ‘yan uwansu da aka kora.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG