Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Almundahana bashi da addini ko kabila ko bangare


EFCC: Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa da duk wani almundahana
EFCC: Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa da duk wani almundahana

A harkokin siyasa ko neman aiki ko cin gajiyar wani abu kawunan 'yan Najeriya na rabuwa bisa addini ko kabilanci ko bangaranci amma ba a cin hanci da rashawa ba.

Muryar Amurka ta zanta da Alhaji Abdullahi Garba Abbas tsohon shugaban karamar hukumar Giwa dake jihar Kaduna wanda ya bayyana yadda 'yan siyasa ke anfani da addini da kabilanci da bangaranci domin cimma muradun kansu.

Yace da zara ana batun siyasa sai 'yan siysa su kawo son rai ba domin cigaban al'umma ko kasa ba.

Badakalar da ta bullo ta hannun Sambo Dasuki tsohon mai ba shugabankasa shawara akan harkokin tsaro ta nuwa kowa da kowa na ciki. Wadanda aka ambata yanzu sun hada da musulmai da kiristoci da 'yan arewa da 'yan kudu da na gabas da na yammacin kasar.

To saidai saboda barkewar badakalar yanzu 'yan Najeriya sun fara ganewa cewa 'yan siyasa na anfani dasu ne su cimma muradunsu. Amma yanzu dan Najeriya ya san hakkinsa ba kamar yadda ake yi a baya ba cubuguzum kawai wani ya zo ya shirya zancen banza zancen wofi.

Zaben 2015 ya nuna inda kowa ya nufa. Mutane suna jin dadin abubuwan dake faruwa akan yaki da cin hanci da rashawa.A karkashin jagorancin shugaba Buhari idan har aka cigaba da haka an kawo karshe.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:04 0:00

XS
SM
MD
LG