“Magana ce suka yi ta a kotu, kuma a kotu an tambaye su yaushe aka fara zarginnan, ba bayani. A ina aka fara zargin, ba bayani. Yaushe aka fara alaqar, babu wata magana. Kuma alkalin ya fada a hukuncinsa, yace wannan karyace kawai, babu ma wani abunda ya kawo wannan maganar, banda cewa sun karbi Fassfo, kuma suna neman wata hujja,” inji Mr. Lamido.
Dan asalin Jihar Kano ya kara da cewa a matsayinsa na dan Najeriya, zai cigaba da yin sharhi, da kuma tsokaci akan al-amuran da suka shafi kasa, kamar yadda ya saba tun kafin ya zama gwamnan Babban Bankin Najeriya.
“Ban yi shiru ba a rayuwata, duk abinda ya kamata a yi magana akai, za’a yi magana akai,” inji Mr. Lamido.