Shi kansa Bukola Saraki ya shigo APC ne daga barakar sabuwar PDP a zamanin mulkin Bamanga Tukur, tabbas dadewar wadanda suka taba yin PDP kan madafun iko ya basu dabarun tasiri a sabuwar majalisar.
Sabon ‘dan majalisar wakilai Ustaz Yunus da yafi kusan kowa dagewa wajen bijirewa bukatun jam’iyyar sa ta APC yace matakin da suka ‘daukan ba tawaye bane. Inda yace, “bamu da rinjayen da zamu iya cin gashin kanmu a majalisa, dole ne sai mun hado da PDP yadda zamuyi su sake damu.” Ya dai ci gaba da zargin jam’iyyar APC na cewa tayi amai ta lashe, tunda tace bazata sa baki ba, daga baya kuma kwatsam ta tsoma bakin ta, basu san da haka bane lokacin da shugaba Buhari ya fito yace duk wanda aka zaba zai yi aiki da shi.
Shi kuma tsohon ‘dan majalisar wakilai Abdrurrazak Zaki wanda yace guguwar Buhari ce ta kawar da shi, yace da alamu APC bata koyi darasi da ga akasin da ya sami jam’iyyar PDP a shekara ta 2011 bane da ya kawo zaben Tambuwal da tura bukatar ta zaben Molikat Adewola.
Saukin da za’ace APC ta samu shine Bukola da Dogara duk ‘yan jam’iyyar ta ne, da asarar bata zama ga mari ga tsinka jaka ba.
Saurari rahotan.