Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da dokar rufe kafofin shiga Jihar Kano daga sassan Najeriya zata fara aiki da karfe 12 na daren Juma’a 28 ga watan Maris.
Alhaji Sani Lawan, dake zaman shugaban kungiyar tashar mota ta Na’ibawa a Kano, ya ce sun shirya tsaf domin tunkarar wanan kalubale. Ya kuma yi kira ga gwamnati da sauran masu hannu da shuni da su taimaka wa masu karamin karfi.
Ga alama wannan doka ta fara tasiri, domin kuwa al’amura sun fara tsayawa cik a tashoshin motar Kano. Duk da cewa, a yau ne dokar hana shiga Kaduna ta fara aiki, ana ci gaba da yin lodin Kaduna da sauran garuruwa daga Kano.
Yayin da ‘yan Najeriya ke bayyana aniyar su ta bada hadin kan da ya kamata ga matakan da hukumomi ke dauka akan wannan annoba ta coronavirus, galibin mutane suna fargabar makomar abin kaiwa bakin salati a karkashin wannan yanayi.
Ga karin bayani cikin sauti.