Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akalla Mutane 12 Suka Rasu a Wani Hari a Tunisia


Wurin da motar safa ta tarwatse a birnin Tunis na kasar Tunisia
Wurin da motar safa ta tarwatse a birnin Tunis na kasar Tunisia

Akalla mutane 12 suka rasu jiya Talata a babban birnin kasar Tunisia yayin da wata motar safa dake dauke da sojoji na musamman na fardar shugaban kasa ta tarwatse inji Ministan Tsaron Cikin Gida.

Bam da ya tarwatsa motar ya tashi ne yayin da motar ke kan wani titi dake da jerin bishiyoyi a tsakiyar Tunis.

Jami'an tsaro da kafofin hukumomin fadar shugaban kasa sun ce hari ne aka kai amma sun kara da cewa ba'a sani ba ko bam ne ko kuma wani abu ne aka jefawa motar yayinda take tafiya akan titin Mohamed V Avenue. Motocin daukan marasa lafiya daga jami'an tsaro sun ruga kafin jami'an tsaron su killace wurin.

Shugaba Beji Caid Essebsi nan take ya kafa dokar ta baci ta kwana talatin a duk fadin kasar tare da dokar hana fitar dare a yankin Tunis. Ya kira taron gaggawa na hukumar tsaro yau Laraba da safe..

Shugaban yace "Ina son na tabbatarwa al'ummar Tunisia cewa zamu murkushe ta'adanci"

Wannan lamarin ya faru ne kwana 10 bayan da hukumomin kasar suka kara daga tsaro a babban birnin kasar tare da kara dakaru masu yawan gaske.

Tun farkon wannan watan jami'an Tunisia suka sanarda tarwatsa wasu da suka ce suna shirin kai hare-hare kan ofisoshin 'yansanda da otel otel a birnin Sousse dake gabar teku mai tazarar kilomita 150 daga Tunis

XS
SM
MD
LG