Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewa an gurfanar da dalibin nan Muhammad Aminu da ake zargi da bata sunan uwargidan shugaban kasa a gaban kuliya.
An gurfanar da Muhammad ne a babbar kotu ta 14 da ke birnin tarayya a ranar Talata a cewar jaridar Daily Nigeria ta yanar gizo.
Ana kuma tuhumar shi ne kan laifukan da suka shafi bata suna.
A kwanakin da suka gabata jami’an tsaro, suka kama Mohammad, dalibi a Jami’ar Tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa, bayan da aka zarge shi da wallafa wani rubutu da ya yi batanci ga Aisha Buhari.
Bayanai sun yi nuni da cewa, yayin zaman kotun, Muhammad ya ki amsa cewa ya aikata bai daidai ba, kuma kotun ta tura shi gidan yarin don a ci gaba da tsare shi kafin a ci gaba da sauraren karar.
A kwanakin baya ne aka zargi Muhammad da wallafa wani rubutu a shafin Twitter da ke nuna cewa “su mama an ci kudin talakawa an koshi” hade da hotonta, lamarin da ya sa jami’an tsaron farin kaya suka yi masa dirar mikiya a jami’ar da ke Dutse, suka tusa keyarsa zuwa Abuja.
Gabanin gurfanar da shi a kotu, rahotanni sun nuna cewa an ci zarafinsa ta hanyar doka, lamarin da ya janyo suka daga sassan Najeriya da dama.
Kungiyar Amnesty Internaitaional a ranar Litinin ta yi Alla-wadai da matakin kama Muhammad inda ta yi zargin an take mai hakkinsa na bil adama.
Har izuwa lokacin hada wannan rahoto, uwargidan shugaban kasa da jami’an tsaro ba su ce uffan kan wannan batu ba.
Muhammad dalibi ne da ke zangon shekara ta karshe, yana kuma shirin rubuta jarabawarsa ta karshe a ranar 5 ga watan Disamba.