Wannan shine karo na 17 da ake yiwa jami'an kiyaye zaman lafiya a kasar irin wannan zargi cikin watanni 17 da yara da shekarunsu ya kama daga 11.
Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a kasar mai lakabin MINUSCA ya fada jiya Talata cewa, zargi na baya bayan nan ya auku ne ranar Asabar data shige.
Wata sanarwa daga ofishin tayi Allah wadai da duk wani "mataki na nuna fin karfi a yi lalata da yara da ake zargin jami'an da suke aikin kiyaye zaman lafiya.
Sai dai sanarwar bata bada wani karin bayani ba, kuma bata bayyana ainihin kasar da wanda ake zargin ya fito ba. Sanarwar tace an sanarda hukumomin kasar cewa masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun fara gudanar da bincike na cikin gida.
Ofishin Majalisar Dinkin Duniya ya karbi ayyukan kiyaye zaman lafiyan ne cikin watan Afrilu na bara.Nauyin ladabtar da wadanda ake zargi yana kan kasashen da jami'an suka fito.
Ita Majalisar Dinkin Duniya an barta ne da hakkin maida wadanda ake zargin kasashen su na asali.