Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afirka Ta Samar Da Rigakafin mRNA Na Farko Na COVID-19


Kamfanin harhada magunguna na Afirka ta Kudu Afrigen shi ne na farko a nahiyar da ya fara kirkiro rigakafin mRNA na COVID-19 ta hanyar amfani da bayanan hada magani na kamfanin Moderna. Kamfanin na fatan fara gwajin maganin rigakafin a watan Nuwamba.

Afrigen yana daya daga cikin kamfanonin da ke shiga cikin cibiyar da ke samun goyon bayan Hukumar Lafiya ta Duniya don samar da alluran rigakafi ga kasashe masu karamin karfi da matsakaicin kudi. Manajan Daraktan Afrigen, Petro Terblanche ta ce rigakafin na mRNA an yi shi ne da tushen ilimin kamfanin, tsarin shi da kuma mutanen shi.

Manajan Daraktan Afrigen Petro Terblanche
Manajan Daraktan Afrigen Petro Terblanche

"A halin yanzu suna ƙara yin gwaje-gwaje na tantancewa don tabbatar da cewa suna da inganci. Don haka wannan shi ne ma'aunin gwajin farko na cikakken allurar riga-kafin da aka haɓaka," in ji ta.

Terblanche ta ce za su bukaci Moderna da ta ba su lasisin da radin kansu, domin dukkan kamfanonin za su ci moriyar shi, sannan kuma, zai yi amfani ga kasashe masu karamin karfi da matsakaicin kudin da za su yi amfani da wannan fasahar.

Ta kara da cewa suna amfani da sabon maganin ne a matsayin gwajin maganin rigakafi na zamani na biyu wanda har yanzu na cikin matsayin tsarin zane.

Kamfanin Moderna dai bai ce komai ba game da sanarwar Afrigen, amma a karshen shekarar da ta gabata ne aka bayar da rahoton cewa kamfanin ya dakatar da takaddamar ikon mallaka da gwamnatin Amurka kan rigakafin cutar coronavirus.

Terblanche ya amince da goyon bayan masana kimiyya a wasu ƙasashe don aikin Afrigen.

Mukaddashin darekta janar na ma'aikatar lafiya ta kasar Afirka ta Kudu, Dr. Nicholas Crisp, ya yi maraba da labarin ci gaban rigakafin na mRNA.

Haka kuma daraktan shiyya na Hukumar Lafiya ta Duniya a Afirka, Dr. Matshidiso Moeti, ya ce kashi 11% na al'ummar Afirka suna da cikakkiyar rigakafin, kuma kashi 85% ba su sami alluran rigakafi ko daya ba. Ya kara da cewa mutane 239,000 ne suka mutu a Afirka sakamakon kamuwa da cutar.

XS
SM
MD
LG