Shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani ya sanar da cewa ba da dadewa ba gwamnatinsa za ta saki sauran fursunonin mayakan Taliban don taimakawa kokarin samar da zaman lafiya wanda Amurka ke jagoranta a kasar.
Ghani ya fada wa wani taron hadin gwiwa na cibiyar habbaka kudancin nahiyar Asiya wadda ke Wasington tare da cibiyar samar da zaman lafiya ta Amurka cewa gwamnatinsa ta riga ta saki fursunoni mayaka 3,000.
“Ni da abokan aikina mun yanke shawarar sakin karin wasu fursunoni 2,000 cikin dan kankanin lokaci. Za mu sanar da lokacin nan ba da jimawa ba, “in ji shugaban na Afghanistan.
Ghani ya ambaci cewa a halin da ake ciki, wata tawagar 'yan Taliban na birnin Kabul ta na tantance fursunonin kungiyar da aka saki daga gidajen yari, don musayar jami’an tsaron Afghanistan 1,000 da ke hannun ‘yan taliban.
Facebook Forum