Alhaji Sa'adu Bello shugaban hukumar NEMA mai kula da sansanin 'yan gudun hijira dake jihar Adamawa yace sun shirya tsaf domin 'yan gudun hijira kiristoci kimanin dubu biyar su samu su gudanar da bikin.
Yace kamar kullum sukan yi tanade-tanade da zasu ba 'yan gudun hijiran damar gudanar da bikin ba wai ya wucesu ba saboda suna sansanin 'yan gudun hijira. Kokarin shi ne su gudanar da bikin kamar yadda su keyi a gidajensu.
A wannan shekarar ma an tanada masu da abubuwan da zasu ci su sha da kuma yanka da za'a yi masu domin su yi hidima kamar kowa. An basu dama su yi duk irin wasannin da suke son yi.
Kamar NEMA wasu kungiyoyin sa kai su ma sun bada tallafi. Alhaji Abdulkarim Salihu babban sakataren kungiyar dake yaki da miyagun kwayoyi yace taimakawa 'yan gudun hijiran nada mahimmanci musamman a wannan lokcin. Sun lura cewa mata da yara aka fi sayawa sutura lokacin bikin kuma su ne suka fi tagayyara a rikicin Boko Haram.Saboda haka sun tanadi kaya da suka raba domin bikin.
Ga karin bayani.