Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Wadanda Suka Rasu A Harin Yola Ya Karu


Mutane suna kallon barnar da aka yi a harin da aka kai wani masallacin Maiduguri, Nigeria, Oct. 23, 2015.
Mutane suna kallon barnar da aka yi a harin da aka kai wani masallacin Maiduguri, Nigeria, Oct. 23, 2015.

Adadadin wadanda suka mutu sakamako harin kunar bakin wake da aka kai a masallacin Jumma’a da ke Jambutu a Yola fadar jihar Adamawa ya haura talatin da uku

Mutane casa’in da shida jinya na jinya a halin yanzu a asibitin kwararru da cibiyar kiwon lafiya na gwamnati tarayya da ke Yola. Hukumomin asibiti sun ba da alkalmar ne lokacin da tawagar da sakataren gwamnatin tarayya Mr, Babacir David Lawal suka kai masu jaje.

A hirar da wakilin Sashen Hausa Sanusi Adamu ya yi da sakateren gwamnatin tarayya Mr, Babacir David Lawal jim kadan bayan ziyarar jaje da ta ta’aziyya da ya kai wa wadanda harin kunar bakin waken ya rutsa da su da gwamnati jiha a asibitin kwararu da cibyar kiwon lafiya ta tarayya. Ya fada cewa akwai bukatar jama’a su farga da irin miyagu ko bata gari da ke zaune tare das u domin gudun kada su cutar da su.

Yace wani lokaci sakacin al’umma ne ke sawa bata gari su shige cikin jama’a suna tada hankali. Ya kuma yi kira garesu su dauki kansu a matsayin jami’an tsaro su rika sanar da hukumomi duk wani taken taken da basu yarda da shi ba,

Yace gwamnatin tarayyar Najeriya a shirye take ta taimakawa gwamnatin jihar Adamawa, domin ganin majinyatan sun sami kyakkyawar kulawa.

Ga cikakken rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:32 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG