Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Wadanda Suka Mutu A Harin Giwa Ya Kai 40


Gwamnan Kaduna Malam Nasiru El Rufai (Facebook/El Rufai)
Gwamnan Kaduna Malam Nasiru El Rufai (Facebook/El Rufai)

A karshen makon da ya gabata ne ‘yan fashin daji suka far wa kauyukan Giwa suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama

Rahotanni daga jihar Kadunan Najeriya na cewa adadin mutanen da hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a yankin karamar hukumar Giwa ya kai 40 cif.

Hakan ya biyo bayan karin gawarwaki biyu da aka gano a ranar Litinin.

A baya hukumomin jihar sun ce adadin ya tsaya ne akan mutum 38 da ‘yan bindigar suka harbe har lahira a kauyukan Kauran Fawa, Marke da Riheya da ke karamar hukumar ta Giwa.

Amma gidan talabijin na Channels ya ruwaito kwamishinan cikin gidan da tsaro Samuel Aruwan yana cewa an samu karin gawar mutum biyu.

A karshen makon da ya gabata ne ‘yan fashin daji suka far wa kauyukan suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Kazalika sun kona gidaje da kadarorin al’umar yankunan.

Hare-haren sun janyo Allah wadai a sassan Najeriya wacce arewacinta ke fama da matsalar tsaro musamman a yammacin yankin.

A ranar Lahadi fadar shugaban kasa ta bayyana alhininta bisa wannan al’amari inda ta ce dakarun kasar na kara kaimi wajen kakkabe ‘yan bindigar da suka addabi yankin.

XS
SM
MD
LG