Yayin da adadin wadanda suka kamu da coronavirus a duniya ya kai kusan miliyan 11.5, gwamnatoci suna ta fadi tashin ganin yadda za su sake farfado da tattalin arzikinsu, lamarin da ya sa wasu daga cikin kasashen sake maido da dokokin kulle ko janye matakan sake maido da harkokin yau da kullum da suka fara dauka.
A jiya Litinin jami’ai a Australia sun sanar da rufe kan iyaka tsakanin Victoria da New South Wales, jahohi biyu da suka fi yawan jama’a a kasar, bayan hauhawar sabbin wadanda suka harbu.
Matakin rufewar da babu ranar budewa, shi ne irin sa na farko a Australia tun bayan lokacin annobar cutar mura da aka gani shekara 100 da suka gabata.
Ita ma Isra’ila jiya Litinin ta sanar da rufe wuraren sayar da barasa, gidajen rawa, wuraren yawon dare da na motsa jiki da kuma wuraren da ake yin ninkaya saboda karuwar wadanda suka kamu a cikin kasar.
Wanann kuma zai rage yawan masu zuwa gidan sayar da abinci da wuraren ibada. Kasar dai tana da wadanda aka tabbatar sun harbu sama da mutum dubu 30,000 da kuma sama da dari mutum 330 da suka mutu.
A nan Amurka an sake maido da dokokin da aka saka na dakile yaduwar cutar a jihohin Texas da Florida saboda yaiwatar masu kamuwa da cutar ta COVID-19.
Facebook Forum