A cikin wata sanarwa da rundunar 'yan sandan jihar ta Zamfara ta fitar ta hanyar kakakin ta SP Mohammed Shehu, ta ce an tabbatar da sace dalibai 317 a farmakin na makarantar sakandaren ta Jangebe.
Sanarwar ta ce tuni da jami’an tsaro da suka kumshi sojoji da ‘yan sanda, sun soma aikin hadin gwiwa na neman daliban.
“Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara CP Abutu Yaro da kwamandan rundunar wanzar da zaman lafiya ta Operation Hadarin Daji, Manjo Janar Aminu Bande, da kwamandan Birget ta daya ta sojin Najeriya da ke Gusau, da sauran manyan jami’an tsaron gwamnati, sun jagoranci wani kakkarfan ayarin jami’an tsaro zuwa Jangebe, domin karfafa aikin ceto yaran a wuraren da ake hasashen an tafi da su.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bukaci shugaba da malaman makarantar har ma da iyayen yaran, da su kwantar da hankalinsu, a yayin da hukumomi ke ci gaba da kokarin tabbatar da kubutar da yaran da aka sace.
Karin bayani akan: Mohammed Adamu Abubakar, jihar Zamfara, Nigeria, da Najeriya.