WASHINGTON, DC —
Rassan Jam’iyyun ANPP da ACN da CPC na jihar Jigawa sun amince su dunkule domin tabbatar da kafuwar sabuwar Jam’iyyar APC a matakin jihar. Shugabanni da kuma wadanda suka yiwa jam'iyun uku takarar gwamna a zaben shekarar dubu biyu da goma sha daya ne suka hallara a Kano domin shiga inuwar APC da ake shirin kafawa. Bayan sun gama taron, wakilin Sashen Hausa a Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya fara da tattaunawa da Honorable Faruk Adamu Aliyu wanda ya nemi kujerar gwamnan jahar Jigawa a karkashin laimar CPC:
ACN Da ANPP Da CPC Na Jigawa Sun Yi Taron Hadewa

Ressan jam'iyun hamayya na ANPP da ACN da CPC na jahar Jigawa sun yi taro a Kano game da narkewa su zama jam'iya daya ta APC