WASHINGTON, DC —
Wakilin Sashen Hausa a jahar Adamawa ya hada ma na rahoto akan wahalhalun rayuwa a jahohin da ke cikin dokar ta baci. Gwamnan jahar Adamawa Murtala Nyako yayi jawabin godewa al'ummar jahar saboda halin hakuri, da juriya da bin doka da suka nuna a wannan mawuyacin lokaci da su ka samu kan su a ciki, sannan gwamnan ya yi zargin cewa duk da wannan ukuba da ake ciki, yanzu haka wasu 'yan jahar ta Adamawa na Abuja su na kumbiya-kumbiyar shawo kan shugaba Goodluck Jonathan ya rike kudaden gudanarwar da ake baiwa jahar Adamawa ta yiwa jama'a aiki. Gwamna Murtala Nyako ya ci gaba da cewa:
Jahohin Adamawa da Borno da Yobe Na Cikin Ukuba

Matsalolin rayuwa na kara tabarbarewa a jahohin da aka kwakubawa dokar ta baci