Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tanadin Doka Kan Amfani Da ‘Yan Ta’adda A Lokacin Zabe


Sakamakon zabe
Sakamakon zabe

A duk lokacin aka buga gangar siyasa a Najeriya, gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu suke fara hada karfi da karfe wajen wayar da kan matasa da kuma yi musu gargadi  da kada  su bari ayi amfani da su wajen tayar da tarzoma a lokacin zabe, tare da yin nuni da irin illolin da ke tattare da hakan.

ANUJA, NIGERIA - Sai dai kuma duk da wannan kokari, akan samu ‘yan ta’adda ko masu tada tazorma a duk lokacin da ake gudanar da zabe ko bayan zaben.

Wannan matsalar dai ta zama abun damuwa, yadda wasu ke kallon hakan a matsayin rashin ilimi ko rashin sanin ya kamata ko kuma rashin bin dokokin kasa da na zabe.

Jami’a a sashen yada labarai na hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, INEC, Zainab Aminu Abubakar ta yi karin bayani game da dokar hukumar wacce ta yi haramcin tada zaune tsaye a lokacin zabe dama baya zaben.

Ta ce "dokokin zabe sashe na 123 zuwa 128 sun yi bayani cewa duk wanda aka samu da tunzura wasu akan wani dan takara ko wata jam’iyya ko neman canzawa mutane ra’ayi ko magana da kalaman batanci, za’a ci shi tarar kudi naira 500,000 ko zaman wata 12 a gidan yari. Haka kuma idan aka samu mutum da wasu ‘yan ta’adda ko kuma wasu gungun mutane sun bata kayan zabe ko kawo hargitsi a lokacin zabe, shi kuma hukuncin zaman wata 24 ne a gidan yari."

Ta kara da cewa "idan kuma aka samu wasu mutane sun dauke ma’aikatan zabe ko kayan zabe hukuncin shined tatar nera miliyan uku ko zaman shekara 3 a gidan yari."

Baya ga dokar zab,e akwai kuma dokar kasa da ta yi magana akan irin wannan laifi kamar yadda mai sharhi kan lamuran shari’a, dimokradiyya da kuma diflomasiyyar duniya, Barista Mainasara kogo Umar ya bayyana.

Masanin kimiyar siyasa na jami’ar Abuja Dr. Farouk B.B. Farouk ya dora alhakin hakan kan ‘yan siyasar kasar, inda yace rashin siyasar akida ko manufa da son zuciya na daga cikin dalilan da yasa ‘yan siyasa a Najeriya ke amfani da ‘yan ta’adda a lokacin zabe.

A nasa bangaren, mai sharhi kan lamuran yau da kullum Aliyu Shamaki y ace ba za'a sami gyara a dimockradiyyar Najeriya ba har sai hukumar zabe ta jajirce wajen tabbatar da doka akan masu tunzura mutane wurin ta’addanci da zubar da jini a lokacin yakin neman zabe.

Za’a iya cewa an gina Najeriya akan dokoki, sai dai masana na cewa kasar na fuskantar kalubalen rashin bin doka da hakan ke haddasa matsaloli a fannoni da dama wajen tafi da kasa.

Saurari cikakken rahoto daga Hauwa Umar:

Abinda Doka Tace GAme Da AMfani Da ‘Yan Ta’adda A Lokacin Zabe.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG