Dakatarwar da ta biyo bayan hudubar sallar jumma’ar makwan jiya, ta haddasa suka mai tsanani, musamman a kafafen sadarwar yanar gizo.
Sheikh Nuru Khalid, wanda ya bukaci jama’a kar su fito zabe matukar ba a inganta tsaro gabanin zaben ba, ya gamu da matakin kwamitin masallacin inda hatta tafsirin da ya saba na Ramadan, aka nada wani limami ya maye gurbinsa.
Khalid da kan shirya shan ruwa da mabiya addinin kirista a masallacin don karfafa fahimtar juna tsakanin addinai, na daukar salon wa’azin kowa ya zo a tafi tare, ko ma a daina mayar da hankali kan batun bidi’a a rika karfafa batun tabarbarewar tsaro.
Limamin masallacin ZONE B na unguwar ‘yan majalisar, Ibrahim Auwal Usama, ya so shiga tsakani kan barazanar tsige Dansadau daga kujerar don samun dawo da Sheikh Khalid da a ke yi wa taken “DIGITAL IMAM” don yanda ya kan yi amfani da na’ura mai kwakwalwa kan mukaminsa.
In za a tuna a sallar idin azumin bara, an samu irin wannan takaddama tsakanin Imam Usama da Dansadau, yayin da Dansadau din ya yi wuf ya karbe na’urar magana ya musanta sukar gwamnatin Buhari da a ke yi cewa ba ta tabuka abun kirki ba. Tunzura da jama’a su ka yi kan ra’ayin Dansadau ya sa ya ce haka aka yi wa Annabawa.
Imam Usama ya sa an yi zaben marawa ra’ayinsa baya ta hanyar kabbara har sau uku, inda jama’a su ka goyi bayan cewa gwamnatin ta gaza.
Unguwar dai da a tarihi ta ‘yan majalisa ce, amma yanzu ta zama kusan gidajen tsoffi da wasu ‘yan majalisa masu ci, tun sayar da gidajen da gwamnatin Obasanjo ta yi a dambarwar tazarce gabanin zaben 2007.
Ga rahoton Nasiru Adamu El Hikaya daga Abuja: