A yayin taron hadin gwiwa da sarakunan gargajiyar yankin da ya gudana a jihar Kaduna, gwamnonin arewacin Najeriya 19 suka bayyana matsayarsu game da batun tsarin karba-karba da wajibcin maida shugabancin kasar zuwa kudanci batun da a baya suka ce hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa.
Yankin kudancin kasar na fadin ya zama wajibi shugbancin kasar ya koma bangarensu, yayin da wasu daga cikin shugabannin Arewa ke cewa kundin tsarin mulki bai tsara hakan ba.
Gwamnan jihar Filato, Samon Lalong ya ce yayin da wasu gwamnonin Arewa ke ganin lokaci ya yi a mayar da mulki kudu, amma taron da shugabannin suka gudanar sun yanke shawarar cewa hakan ya sabawa tsarin mulkin Najeriya, domin tsarin mulki bai tilastawa kowa ya yi zabe ba.
Barrista Mainasara Kogo Umar, ya ce maganar karba-karba batu ne na san rai amma taken Najeriya ya bayyana cewa hadin kan kasa da girmama bangarori daban-daban shi ne zai kawo ci gaban al’umma.
A wani bangaren kuma wasu na ganin duk da cewa mulkin na karba-karba ba ya cikin kundin tsarin mulki, tsarin zai iya samar da daidaito wajen samar da zaman lafiya da kore rarrabuwar kawunan al'umomin kasar.
A 'yan watannin baya kungiyar gwamnonin kudancin Najeriya suka yi taro a jihar Legas inda suka cimma matsaya cewa shugabanicn kasar ya koma yankinsu.
Domin karin bayani saurari rahotan Halima Abdurra’uf.