Hukumomin kasar dai ba su ambaci sunan matar ba, amma sun ce an haife ta ne a shekarar 1992, ta kuma zauna a gabashin birnin Kars da ke Turkiyya, sannan daga baya ta shiga kungiyar PKK da aka haramta a shekarar 2013.
Wannan hari da aka kai ranar Lahadi a dandalin Kizilay da ke Ankara, an kai shi ne a wani babban wajen hada-hadar kasuwanci da sufuri, kuma shi ne na biyu mafi muni a jerin hare-haren da aka kai a watan da ya gabata, wanda hukumomin kasar ke dora alhaki akan mayakan Kurdawa.
Su dai mayakan na Kurdawa sun kwashe shekaru kusan 30 suna fada da dakarun kasar a wani mataki na neman ‘yancin kansu a kudu maso gabashin kasar.
Akalla mutane 210 suka rasa rayukansu a hare-haren kunar bakin waken da ake zargin kungiyar ta mayakan Kurdawa ko kuma mayakan IS da kaiwa.
A halin da ake ciki yanzu, Shugaban kasar ta Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya sha alwashin ganin bayan duk wata kungiyar ‘yan ta’adda na kasar.