Mataimakin darakta a ma'aikatar kula da muhalli ta tarayyar Najeriya Mr. Ben Bengun yace sun yi nazari mai zurfi tare da bincike akan sauyin yanayi da kasar ta gabatar a taron kolin da aka yi a Paris babban birnin Faransa.
Binciken wani bangare ne na nuna hobbasa da kasar ta keyi akan sauyin yanayi.Yana kuma cikin kokarin da kasar keyi domin dakile saujin yanayi a duniya.
A kan matsalar sauyin yanayi a Najeriya Mr. Ben yace lamarin abun juyayi ne a Najeriya. Yana bukatar duk masu ruwa da tsaki a batun muhalli su tashi tsaye su yi wani abu cikin gaggawa.
Tun farko hukumar harsashen yanayin a Najeriya tayi harsashen cewa damina zata yi jinkiri kana kaka zata shigo da wuri sabanin yadda aka saba gani. Ruwa yayi jinkirin zuwa kuma ranar 30 ga watan Oktoba ya tsaya. Wannan zai shafi nagartar anfanin gona. Duk wannan matsalar sauyin yanayi ya jawoshi.
Dr. Amina Zakari likita ce a ofishin babban birnin tarayyar Najeriya. Tace idan ba'a dakatar da sauyin yanayi ba ciwon daji musamman na fatun jikin dan Adama zai karu. Hatta ruwan sama da ke taimakawa mutum zai zama da lahani idan aka samu sauyin yanayi. Abubuwan da ya kamata ruwan ya kawar daga jikin mutum ba zai kawar ba sai su koma cikin jinin mutum si jawo ciwon daji.
Ga karin bayani.