Mai magana da yawun jam'iyyar RSD Gaskiya Alhaji Hamza Issa, ya bayyanawa Muryar Amurka cewa suna kan bakarsu sai an yiwa kundun tsarin zaben kasar garambawul.
Ya bukaci cewa duk jam'yyun siyasa dake cikin majalisar dokokin kasar ya zamanto suna da wakilai a hukumar zaben kasa wato CENI kada a bar kowace jam'iyya baya.
Abu na biyu inji Alhaji Hamza Issa, saka ma'aikatan gwamnati cikin hukumar zabe ba ya kan kaida saboda ma'aikata ba 'yan siyasa ba ne. Ya ce a kundun tsarin zaben akwai wakilai ma'aikata da aka ce suna cikin hukumar zabe kuma zasu kada kuri'unsu. A cewarsa ya kamata a gyara.
Manufarsu ita ce a yi zabe nagari ta yadda bayan zaben babu wata kura da zata taso.
Dangane da ko gyaran zai bata wa jam'iyya mai muliki, wato, PNDS Tarayya rai, Alhaji Issa ya ce domin an kira a yi gyara ba zai kaiga bacin rai ba saboda aikin kasa ba na mutum guda ba ne. Ya ce Allah yake ba da mulki kuma yanzu ba'a san wanda zai karbi mulki ba a shekarar 2021. Yanzu ya kamata a yi gyara ta yadda kowa zai amince da zaben, injishi.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Facebook Forum