Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Nijar Ta Amince Da Kasafin Kudin 2018 Da Gwamnati Ta Gabatar


'Yan Majalisar Dokokin Niger suna muhawara akan kasafin kudin da gwamnati ta gabatar masu
'Yan Majalisar Dokokin Niger suna muhawara akan kasafin kudin da gwamnati ta gabatar masu

Tun farko 'yan adawa sun yi caa tare da wasu mutanen suna nuna kin wasu matakan da gwamnati zata dauka karkashin kasafin kudin, to sai dai duk da haka, Majalisar Dokokin kasar, cikin tsauraran matakan tsaro, ta amince da shi.

Cikin tsauraran matakan tsaro Majlisar Dokokin Nijar ta yi zamanta jiya Lahadi inda aka girke jami'an tsaro a duk hanayar da ta shiga Majalisar.

To sai dai hayaniya ta barke a zauren Majalisar tsakanin shugaban Majalisar da bangaren adawa saboda zargin da 'yan adawan suka yi masa na nuna bangaranci a lokacin da suke muhawara.

Ministan kudi Hassan Masaudu ya yiwa 'yan Majalisar bayani domin kare hujjojin gwamnati wajen bullo da sabbin haraji wadanda galibinsu matakai ne da ministan ya ce na dede da tsarin harajin bai daya na kasashen kungiyar IRMUWA kafin ya amsa tambayoyi akan wasu matakan da ake gani za su iya jefa talakawa cikin kunci.

A cewar ministan duk abun da aka yi saboda talakawa ne domin an sa za'a gina hanyoyi, a bada ruwa, a kyautata harkokin kiwo da noma da samar da tsaro. Yana ganin kururuwar da 'yan adawa ke yi duk shirme ne.

A karshen muhawarar 'yan Majalisar sun amince da kasafin da kur'u dari da talatin da uku daga cikin dari da saba'in da daya, ke nan talatin da takwas kacal ne suka ki amincewa.

Gwamnatin na sa ran kashe sefa biliyan dubu daya da dari takwas a kasafin kudin badi abun da 'yan adawa suka lashi takobin ci gaba da gwagwarmaya a kansa

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG