Bisa duka alamu za’a shiga takunsaka tsakanin gwamnatin jihar Neja da kungiyar kwadagon jihar dangane da rashin iya biyan ma’aikatanta cikakken albashinsu.
Gwamnatin jihar tace tana fama da karancin kudi a halin yanzu saboda haka abun da ta samu shi zata biya.
Sai dai kungiyar kwadagon jihar ta sanya kafa ta yi watsi da matsayin gwamnatin jihar na cewa zata biya wani bangaren albashin ma’aikatan.
Kwamred Yahaya Idris Ndako shugaban kungiyar kwadagon reshen jihar yace su basu yadda ba. Magana ce da babu ruwansu da ita. Yace kowane ma’aikaci sai an biyashi albashinsa cikakke. Abun da gwamnatin take son ta yi baya cikin alkawarin dake tsakaninsu da ita.
Dangane da dalilin da gwamnati ta bayar na kasa biyan cikakken albashi, Kwamred Ndako yace a rabu da gwamnati. Lokacin da suke pacaka da kudi wa suka gayawa. Su abun da ya damesu shi ne biyansu cikakken albashi.
A kan matsalar gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello ya kira taron masu ruwa da tsaki akan sha’anin mulkin jihar domin tattauna matsalar karancin kudi.
Bayan taron gwamnan ya shaidawa Muryar Amurka cewa ya yiwa mutane bayani akan matsalar karancin kudi. Gwamnan ya bada misali. Yace da jihar tana samun nera biliyan biyar zuwa bakwai daga gwamnatin tarayya kowane wata amma yanzu tana karban nera biliyan daya da miliyan dari biyar ne kawai daga gwamnatin tarayya a wata.
Amma kuma albashin jihar kowane wata ya kama nera biliyan biyu da miliyan dari hudu. A kan albashin ma’aikata, gwamnan yace abun da jihar ta samu da shi zata yi anfani. Idan gwamnatin tarayya ta ba jihar wani agaji za’a karawa ma’aikatan. Gwamnan yace koda ma ma’aikatan basu samu albashinsu gaba daya ba zasu samu kusan duka.
Ga karin bayani.