Gwamnatin jihar tace ta kashe sama da Nera miliyan dari biyu wajen sayo tan dubu daya da dari biyar da tamanin domin sayarwa jama'ar jihar bisa yin la'akari da yadda mutane ke fama da karanci da tsadar cimaka a wannan lokacin.
Mataimakin gwamnan jihar Alhaji Muhammad Keso shi ya bayyana hakan a lokacin fara sayar da abincin wa jama'a a Minna fadar gwamnatin jihar.
Sakataren yada labaran gwamnan Jibril Baba Ndachi ya yi karin haske akan yadda suka tsara sayar da cimakar wa jama'a. Yace idan mudun shinkafa a kasu nera dari shida ne to gwamnan jihar yace a sayar da na gwamnati dari uku, wato rabin abun d a ke sayarwa a kasuwa. Haka za'a sayar da abincin a duk kananan hukumomi 25 na jihar. Inji Baba Ndachi, gwamnan ya roki wadanda aka dorawa alhakin sayar da cimakar da su yi adalci.
A tsarin gwamnati , ta hana a sayarwa kowane mutum buhu daya sukutum saboda ana son kowa ya samu.
Wannan shirin na zuwa ne a daidai lokacin da malamai ke bayyana mahimmancin kaiwa jama'a doki musamman a lokacin Ramadan kamar yadda shugaban gudanarwa na kungiyar IZALA, Shaikh Abdulmuiyi ya ce.
Da alama shirin sayarda abinci da rahusa ya faranta ran wasu mabukata. Wani Salihu Isa yace ya yi murna kwarai da gaske da shirin saboda ya samu shinkafa a rabin farashin da ake sayarwa a kasuwa. Duk mutanen da aka zanta dasu sun bayyana farin cikinsu.
Ga karin bayani.