Korar da mai filin ya yi masu ya sa sun sake fadawa cikin wani halin kakanikayi saboda dukanasu mutane ne da suka baro duk abun da suke dashi baya.
'Yan gudun hijiran sun fito ne daga garuruwan da 'yan Boko Haram suka karbe kafin a sake kwatosu. Amma duk da sake kwato garuruwan dole ne a sake ginasu kafin su iya komawa.
Yanzu dai 'yan gudun hijiran sun fice daga filin domin babu wani ginannen gida ciki. Su ne suka gina rumfunan kara su samu matsuguni amma kuma tare da biyan kudin haya.
Yanzu suna wata anguwa da ake kira Shuwari Madinatu inda suka sake gina rumfuna domin samun wurin kwana kuma mafi yawansu mata ne tare da 'ya'yansu. Wani bawan Allah ne ya basu nashi filin.
Wakilin Muryar Amurka da ya zagaya inda 'yan gudun hijiran suke sun fada masa cewa basa samun taimako daga koina. Hatta ruwan sha sai sun fita su roka kafin su samu wanda zasu sha.
Yanzu kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa domin sake gina arewa maso gabas ya gano wadannan 'yan gudun hijiran kuma ya soma taimaka masu da abinci bayan da wakilin Muryar Amurka ya jawo hankalin mahukunta kan sansanin na wadannan 'yan gudun hijiran
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani
Facebook Forum