Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jamus Kotu Ta Sami Wata 'Yar Kungiyar NAZI Da Laifin Kashe Mutane 10


 Beate Zschaepe wadda ta kashe mutane 10
Beate Zschaepe wadda ta kashe mutane 10

Beate Zschsepe dake zama 'yar wata kungiya dake rajin bin tafarkin Hitler ta kashe bakin haure tara, takwas 'yan asalin Turkiya ne, daya dan Girka da yar sanda daya 'yar Jamus wadanda ta kashe tsakanin shekarun 2000 zuwa 2007

A Jamus, wata kotun kasar ta sami wata 'yar kungiyar rajin wariya ta NAZI masu bin tafarkin Hitler, da laifin kashe kashe har 10, kuma ta yanke mata hukuncin daurin rai-da-rai, bayan da aka kwashe shekaru biyar ana shari'a.

Matar mai suna Beate Zschaepe, itace ta karshe da aka sani a zaman 'yar kungyar da ake kira National Socilaist Underground group, an sameta da laifin kashe bakin haure 9, takwas 'yan kasar Turkiyya, daya daga Girka, da kuma 'Yar sandan kasar ta Jamus. Ta aikata wadannan laifuffukan ne tsakannin shekara ta 2000-zuwa 2007. Masu gabatar da kara suka ce ra'ayinta na wariya shine dalilin kisan kan.

Haka nan an sameta da laifin kai hare hare da bama-bamai har sau biyu a birnin Cologne, tareda fashi har 15,da kuma kasancewar ta 'yar kungiyar ta'addanci.

An kama ta ne a 2011, bayan da 'yan kungiyar ta NSU suka mutu sakamakon kunar bakin wake bayan da wani yunkurin fashi da suka yi ya faskara. Zschaepe, ta kona dakin da suke zama tareda mutanen biyu. Daga baya ta amsa laifin cunnawa dakin wuta da gangan.

Masu gabatar da kara sunyi amfani da wani fefen vidiyo da mutanen biyu suka bari da bayanin ta'asar da suka yi,wajen shari'ar da aka sami Beate da laifi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG